in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalissar dattawan Amurka ta amince da karawa Rasha da Iran da Koriya ta Arewa takunkumi
2017-07-28 10:12:20 cri

Majalissar dattawan Amurka ta amince da wani kuduri, wanda ya bukaci kakabawa wasu sassa na Rasha da Iran da Koriya ta Arewa takunkumi mai tsanani.

Majalissar ta dattijai ta amincewa kudurin da shugaban kasar Donald Trump ya gabatar da gagarumin rinjaye, kwanaki biyu bayan da majalissar wakilan kasar ta amince da shi.

A jiya Alhamis ne dai aka kada kuri'a kan wannan kuduri, inda ya samu amincewa da kuri'u 98, yayin da 'yan majalissar 2 suka ki amincewa da shi.

Baya ga kakaba takunkumi, kudurin dokar ya kuma tanaji wani sashe, wanda zai baiwa 'yan majalissar dokokin Amurkan damar dakatar da shugaban na Amurka, yayin da duk ya yi yunkurin dagewa Rasha takunkumi. Yanzu dai haka ana sa ran aikewa da kudurin dokar fadar White House, domin shugaban kasar ya sanya hannu a kan sa, ko kuma ya kalubalance shi.

Wannan dai mataki na zuwa ne, a gabar da jami'an fadar shugaban kasar ke jaddada bukatar baiwa shugaba Trump damar sarrafa alakar gwamnatin sa da Rasha. Ba a dai tabbatar da matakin da shugaba Trump zai dauka game da wannan doka ba.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China