in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta yi maraba da yarjejeniyar tsagaita bude ta Syria
2017-07-27 19:09:21 cri

Kasar Sin ta bayyana a yau Alhamis cewa, tana maraba da rawar da sassan masu ruwa da tsaki suka taka wajen aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma a yankin da aka shata, bisa la'akari da mutunta 'yancin mallakar cikakakkun yankunan kasar Syria.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Lu Kang wanda ya bayyana hakan, ya ce ya kamata wannan mataki ya taimaka wajen samar da yanayin da ya dace na yayata tattaunawar tabbatar da zaman lafiya a kasar Syria da ake yi a Geneva.

Lu Kang yana wadannan kalamai ne game da rahotanni dake cewa, kasar Rasha ta aike ta dakaru don sa-ido game da yadda ake tsagaita bude wuta a yankunan Syria da aka shata.

A ranar 4 ga watan Mayu ne, kasashen Rasha da Turkiya da Iran suka sanya hannun kan wata yarjejeniyar fahimtar juna game da kafa wasu yankunan mun tsira guda 4 a Syria, da nufin rage zaman zulumi na a kalla watanni 6 a kasar ta Syria.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China