in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Zimmbabwe ya yi kira da tabbatar da zaman lafiya gabanin zabukan kasar
2017-07-27 11:44:52 cri
Shugaban Zimbabwe Robert Mugabe, ya bukaci al'ummar kasar su zauna lafiya gabanin zabukan da aka shirya yi a tsakiyar shekarar 2018.

Robert Mugabe, Ya yi kira da a kauracewa rikicin zabe domin ya na haifar da rashin sahihancin.

Ya ce yayin da ake shirin zabukan 2018, ya na mai bukatar al'ummar kasar su ci gaba da zama tsintsiya madaurinki daya wajen dabbaka zaman lafiya, inda ya ce kada a baiwa masu suka damar illata tsarin dimokaradiyyar su ba..

Har ila yau, shugaban ya ce ya na da yakinin 'yan sanda za su iya aikin da ya dace na tabbatar da zaman lafiya da doka da oda. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China