in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bankin duniya ya baiwa Saliyo tallafin dala miliyan 10 domin inganta harkokin mallakar filaye
2017-07-27 11:38:48 cri
Babban bankin duniya ya baiwa gwamnatin kasar Saliyo tallafin kudi har dalar Amurka miliyan 10, domin inganta harkokin mallakar filaye. Daraktan bankin dake Saliyo Parminder Brar ne ya bayyana hakan a ranar Laraba, yana mai cewa matakin, na da nufin baiwa kasar damar fita daga matsalolin da mallakar filaye ke haifarwa ga al'ummarta.

Mr. Brar ya bayyana hakan ne, yayin bude wani taron karawa juna sani na yini biyu, game da batun mallakar filaye da aka yiwa lakabi da "Mafita game da sauye sauye a fannin mallakar filaye a Saliyo." Ya ce bankin duniya ya damu da wannan lamari ne, duba da tasirin sa ga tattalin arziki da rayuwa, gami da zamantakewar al'ummar Saliyo.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China