A ranar Talatar data gabata, aka hallaka biyu daga cikin jami'an wanzar da zaman lafiyar yan kasar Morocco, kana wani mutum guda kuma ya gamu da raunuka a lokacin wani hari da ake zargin magoya bayan kungiyar anti-Balaka suka kaddamar, kamar yadda MDD ta tabbatar da hakan. Al'amarin dai ya faru ne kwanaki biyu bayan wani makamancin harin da aka kaddamar kan jami'an wanzar da zaman lafiyar 'yan asalin kasar Morocco a birnin na Bangassou a ranar Lahadi, inda mutum guda ya rasa ransa.
Cikin wata sanarwa da aka fitar, Guterres ya bayyana cewa yayi matukar nuna damuwa dangane da tashin hankalin da ya barke a kudu maso gabashin jamhuriyar tsakiyar Afrika, lamarin da ke kara haifar da zaman tankiya sakamakon fadan kabilanci, wanda ke neman ta'azzara shirin zaman lafiya a kasar.