in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin: Za a zabi rukuni na 3 na 'yan sama jannati
2017-07-27 10:22:14 cri
Rahotanni na cewa, nan gaba kadan za a tantance, tare da zabar mambobin rukuni na 3 na 'yan sama jannatin kasar Sin.

Da yake tabbatar da hakan yayin bikin bude baje kolin hotunan ayyukan sama jannati na kasar ta Sin da aka gudanar a jiya Laraba, mataimakin darakta a sashen aikin injiniya na shirin binciken sararin samaniya da kumbuna masu dauke da bil Adama, Yang Liwei, ya ce mambobin rukunin na 3 za su hada da injiniyoyi masu aikin hadawa da kuma kula da na'urori.

Rukuni na farko da na biyu na 'yan sama jannatin dai matukan jiragen saman soji ne na kasar ta Sin.

Game da irin ci gaban da aka samu a aikin bincike a wannan fanni na kimiyya kuwa, Mr. Yang wanda shi ne dan sama jinnati na farko a kasar Sin, ya ce sabbin 'yan sama jannatin na da damar daukar hotuna daga sassa daban daban, da kuma sarari wadatacce na gudanar da ayyukan su.

Ya ce a lokacin da suka gudanar da aikin su can a baya, suna iya daukar hotuna ne kawai ta tagogi biyu na kumbon da suke ciki.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China