in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata kasar da Dalai Lama zai kai ziyara ta tsaida kudurin da ya dace
2017-07-26 18:58:39 cri
Rahotanni na nuna cewa, Dalai Lama zai kai ziyara kasar Botswana a wata mai zuwa. Game da wannan batu, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya bayyana wa taron 'yan jarida a yau Laraba a nan birnin Beijing cewa, batun Tibet batu ne da ya shafi 'yancin mallakar yankunan kasar Sin. Don haka kasar Sin ta bukaci kasar da abin ya shafa da ta martaba muradun kasar Sin, tare da tsaida kudurin da ya dace kan wannan batun. Kasar Sin ba ta tsoma baki a harkokin cikin gidan wasu kasashe, amma ba ta amince wasu kasashe su aikata abin da ya sabawa muradun ta ba. (Zainab)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China