in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mataimakin Firaministan kasar Sin ya bukaci a kara yunkurawa dan kare ambaliya
2017-07-26 11:21:20 cri

Mataimakin Firaministan kasar Sin Wang Yang, ya yi kira da a kara karfafa matakan takaita aukuwar ambaliyar ruwa a kasar, la'akari da shigar lokacin damina.

Da yake bada umarni game da ayyukan rage radadin annoba, Wang yang ya ce zuwan ruwan sama da guguwa a kasar Sin kan sa a shiga matsanancin yanayi, a dan haka ya ce kada gwamnatocin yankuna su yi kasa a gwiwa wajen kare aukuwar ambaliyar ruwa tare da tabbatar da kare al'umma.

Ya ce dole ne hukumomin yankuna su inganta hasashen ruwan sama da ambaliya, tare da wallafa gargadi da wuri da kuma inganta shirye-shiryen kwashe mutane.

Har ila yau, ya ce ya kamata a kara matse kaimi wajen sa ido kan koguna da yankuna masu tsaunuka da kare aukuwar ambaliya a birane, ya na mai cewa gwamnatocin yankuna su ma su shirya tunkarar zaftarewar kasa da mahaukaciyar guguwa kan haifar.

Hukumar kula da yanayi ta kasar ta ci gaba da yin gargadi a jiya Talata, inda ta yi hasashen za a samu guguwar ruwa a wasu sassan arewaci da kudancin kasar. inda yawan ruwan da zai sauka a wasu yankuna zai kai milimita 150.

Wang Yang ya kuma jadadda muhimmanci dake akwai na daukar matakan rage radadin fari a lokacin da ake samun matsanancin zafi a mafi yawan sassan kasar. (Fa'iza Msutapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China