in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar dokokin Amurka ta aza takunkumi mai tsauri kan Rasha, Iran da Koriya ta Arewa
2017-07-26 10:57:57 cri

A ranar Talata majalisar dokokin Amurka ta kada kuri'ar amincewa da babban rinjaye na tsaurara takunkumi kan kasashen Rasha, Iran da Koriya ta Arewa.

Wannan kuduri ya samu gagarumin rinjaye, inda ya samu amincewar kashi biyu bisa uku na kuri'un da aka kada a majalisar dokokin ta Amurka, hakan na nufin majalisar dokokin ta danne bukatar da shugaban kasar Amurkar ke da ita kan wannan batu.

Matakin da majalisar ta dauka tamkar ramuwar gayya ne kan jami'an kasar Rasha game da zargin da ake yiwa Moscown da hannu a zaben shugaban kasar Amurka da aka gudanar a shekarar 2016, da kuma aza takunkumin kan kasashen Iran da Koriya ta Arewa bisa tuhumarsu da shirinsu na gwajin makamai masu linzami.

Shugaban kwamitin kula da harkokin kasashen waje na majalisar dokokin Amurkar Ed Royce, ya bayyana cewa, baki daya kasashen uku sun kasance tamkar barazana ga manufofin Amurkar, kana suna haddasa tada zaune tsaye a makwabtan kasashe. Ya ce lokaci ya yi da majalisar dokokin Amurkar za ta mayar da martini.

Baya ga aza sabbin takunkumin kan kasashen uku, kuduri zai kuma baiwa majalisar damar takawa shugaban kasar Amurka Donald Trump birki na hana shi ikon dagewa Rashar takunkumi. Majalisar ta dauki wannan mataki ne duk kuwa da kira da jami'an gwamnatin mista Trump suka yi ga majalisar dokokin Amurkar, inda suka nemi a yi sassauci bisa la'akari da huldar dake tsakanin Amurkar da Rasha.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China