in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhu ya bukaci Palasdinu da Isra'ila su koma kan teburin shawarwari
2017-07-26 10:23:47 cri

Ranar 25 ga wata, kwamitin sulhu na MDD ya kira wani taro kan batun Palasdinu, inda aka bukaci Palasdinu da Isra'ila da su kai zuciya nesa, su koma kan teburin shawarwari na siyasa cikin hanzari. Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Liu Jieyi, shi ne ya shugabanci taron.

A yayin taron na jiya Talata 25 ga wata, mai shiga tsakani na musamman na MDD wanda ke kula da aikin shimfida zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya Nickolay Mladenov ya sanar da kasashe mambobin kwamitin sulhu, da kuma wadanda suka halarci taron halin da ake ciki a Palasdinu, musamman ma a Kudus a 'yan kwanakin baya."Rikici ya yi kamari a yankin a kwanan baya, inda ake kara fuskantar hadari. Abun da ya abku a tsohon garin Kudus ya girgiza yankin Gabas ta Tsakiya baki daya."

Mladenov ya jaddada cewa, yanzu bai kamata ba sassa daban daban masu ruwa da tsaki su tsokani juna, dole ne su kai zuciya nesa, su yi kokari domin warware rikicin da ake fuskanta yanzu cikin sauri. A cikin jawabinsa, Mladenov ya nuna amincewarsa da matakin cire na'urorin gano makamai daga wuraren shiga wajen ibada mai tsarki da aka fi sani da masallaci mai daraja a tsakanin musulmai, wanda Yahudawa ke kiransa da Temple Mount. Ya kuma kalubalanci Palasdinu da Isra'ila da su koma kan teburin shawarwarin zaman lafiya nan da nan."Rikicin ya hana mu mai da hankali kan ainihin aikinmu, wato yadda za a maido da aikin siyasa, a kokarin taimakawa Yahudawa da Palasdinawa cimma burinsu na kafa kasashensu. Kamata ya yi a cimma burin su bisa kudurorin MDD na masu ruwa da tsaki, kana bangarorin 2 su yi shawarwari a tsakaninsu, ta yadda a karshe kasashensu 2 za su iya zaman tare cikin lumana."

Zaunannen dan kallo na Palasdinu a MDD da kuma zaunannen wakilin Isra'ila a MDD dukkansu sun halarcin taron. Zaunannen dan kallo na Palasdinu a MDD kuma ya yaba wa kasar Sin shirya wannan taro, a matsayin shugaban kwamitin sulhu a zagaye-zagaye.

Mista Liu Jieyi, zaunannen wakilin kasar Sin a MDD ya bayyana cikin jawabinsa cewa, kamata ya yi kasashen duniya su yi hangen nesa, su kara azama kan warware batun Palasdinu a siyasance baki daya da kare halaltattun hakkokin Palasdinawa bisa tunanin kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Gabas ta Tsakiya da ma duk duniya, sa'an nan su yi kokarin hana lalacewar halin da ake ciki a Palasdinu da Isra'ila da ma yankin Gabas ta Tsakiya baki daya."Kwanan baya, halin da ake ciki a Kudus ya tabarbare. Abun da ya zama dole a yi yanzu shi ne sassauta halin fito-na-fito da ake ciki, sakamakon batun masallacin al-Aqsa, kuma a cimma daidaito kan yadda za a sanyaya halin da ake ciki yanzu cikin hanzari, a kokarin hana rikicin yin kamari. Kamata ya yi kwamitin sulhu da kasashen da ke yankin Gabas ta Tsakiya su dauki matakan gaggawa na diplomasiyya, su yi iyakacin kokarinsu wajen gudanar da ayyuka masu alaka, su kwantar da kura cikin sauri, a kokarin hana rikicin ya kara yin illa a wasu wurare na daban. Har ila yau kuma, wajibi ne a aiwatar da kudurorin kwamitin sulhu da abin ya shafa, ciki har da tabbatar da yadda birnin Kudus yake yanzu. Mun lura da matakin da Isra'ila ta dauka a yau, wato cire na'urorin gano makamai daga wuraren shiga wajen ibada mai tsarki na da aka fi sani da masallaci mai daraja a tsakanin musulmai, yayin da Yahudawa ke kiransa da Temple Mount. Muna fatan sassa daban daban masu ruwa da tsaki za su ci gaba da tuntubar juna, da tattaunawa a tsakaninsu, a kokarin kwantar da kura nan da nan. Kasar Sin tana son ci gaba da yin kokari tare da su wajen karfafa gwiwar Palasdinu da Isra'ila da su daidaita batun yanzu da maido da shawarwarin zaman lafiya ba tare da bata lokaci ba, a kokarin warware batun Palasdinu da Isra'ila baki daya cikin adalci da sauri, ta yadda za a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Gabas ta Tsakiya." (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China