Mr.Liu Jieyi ya bayyana ra'ayoyin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar a kwanan baya game da daidaita batun Palasdinu, wato na farko, a daidaita batun a siyasance bisa shirin "kasancewar kasashe biyu". Na biyu kuwa, a tsaya kan manufar hadin gwiwa da juna da samun tsaro mai dorewa. Na uku, a daidaita kokarin kasa da kasa, don kara hada karfin kasa da kasa a wajen wanzar da zaman lafiya a shiyyar. Sai kuma na hudu,
a wanzar da zaman lafiya ta hanyar samun ci gaban shiyyar.
Mr.Liu Jieyi ya ce, kasar Sin ta gabatar ra'ayoyin hudun ne bisa yanayin da ake ciki, kuma kokari ne da kasar ke yi game da daidaita batun Palasdinu, haka kuma manufa ce da kasar ke bi wajen daidaita batun a mataki na gaba.(Lubabatu)