in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cutar gudawa ta yi sanadin mutuwar mutane 2 a Nijeriya
2017-07-26 09:23:24 cri

Kwamishinan lafiya na jihar Lagos Jide Idris, ya ce cutar gudawa ta yi sanadin mutuwar mutane biyu daga cikin mutane 27 da suka kamu da ita a jihar dake a matsayin cibiyar kasuwanci ta kasar, a daidai lokacin da aka kara daura damarar takaita yaduwar cutar.

Yayin wani taron manema labarai da ya gudana a jiya, Jide Idris ya alakanta barkewar cutar da ambaliyar ruwa da aka fuskanta a wasu sassan jihar, biyo bayan mamakon ruwan sama da aka yi cikin 'yan kwanakin da suka wuce.

Kananan hukumomin da aka samu barkewar cutar sun hada da Shomolu da Oshodi-Isolo da kuma Surulere . (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China