in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakatare janar na MDD ya yi tir da harin da aka kai sansanonin 'yan gudun hijira a Nijeriya
2017-07-26 09:20:12 cri

Sakatare janar na MDD Antonio Guterres ya yi tir da kakkausar murya kan hare-haren kunar bakin wake da aka kai sansanoni biyu na 'yan gudun hijira a birnin Maidugurin jihar Borno dake arewa maso gabashin Nijeriya.

Harin da wasu mata 2 'yan kunar bakin wake suka kai ranar Litinin da ta gabata kan sansanonin 'yan gudun hijira dake kusa da birnin Maiduguri, ya yi sanadin mutuwar a kalla mutane 7 yayin da wasu 15 suka jikkata.

Wata sanarwa da aka fitar, ta ruwaito Antonio Guterres na yin kira da a hukunta wadanda ke da alhakin kai harin ta'addancin, inda ya jadadda goyon bayan MDD ga gwamnatin Nijeriya a yaki da take da ayyukan ta'addanci da tsatsauran ra'ayi. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China