in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yiwa sojojin Najeriya sama da 6,000 karin girma
2017-07-26 09:13:46 cri

Rundunar sojin Najeriya ta daga matsayin wasu dakarun ta su 6,199, bisa kwazo da suka nuna, a fafatawar da suke yi da kungiyar nan ta Boko Haram a sassan arewa maso gabashin kasar.

Babban hafsan sojojin Najeriyar Laftana Janar Tukur Buratai ne ya amince da karin girman da aka yiwa sojojin zuwa mukamai daban daban.

Da yake karin haske game da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar, kakakin rundunar sojin kasar Birgediya Janar Sani Usman, ya ce an daga matsayin wasu saja su 329 zuwa warrant officer, da wasu saja su 371 zuwa staff saja. Kaza lika an daga likkafar wasu kofur su 707 zuwa matsayin saja.

Sauran sun hada da kananan kofur 1,290 da aka daga matsayin su zuwa manyan Kofur, da kuma wasu Private su 3,502 da aka yiwa karin matsayi zuwa kofur.

Sanarwar ta rawaito Laftana Janar Buratai na taya sojojin da suka samu karin matsayin murna, yana mai jan hankalin su da su matsa kaimi wajen fatattakar mayakan Boko Haram a daukacin yankin arewa maso gabashin Najeriya.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China