in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya na shirin bunkasa kayan gwajin harbi na dakarunta
2017-07-26 08:55:59 cri

Rundunar sojin saman Najeriya ta ce, ta samar da sabbin na'urorin gwajin harbin bindigogi guda uku, domin inganta ayyukan horo na dakarun ta. Shugaban rundunar dakarun sojin saman kasar Air Marshal Sadiq Abubakar ne ya tabbatar da hakan jiya Talata a garin Bauchi, yana mai cewa, na'urorin na zamani, na cikin sabbin kayan aikin soji da ake alfahari da ingancin su yanzu haka a sassan duniya.

Abubakar wanda ya halarci kaddamar da sabon sansanin gwajin harbin bindigogi na rundunar ta sa a jihar Bauchi, ya ce tuni suka kafa makamancin sa a jihar Kaduna dake arewacin kasar, yayin da kuma ake shirin kafa karin wani sansanin a birnin Fatakwal na jihar Rivers dake kudancin kasar.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China