in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Habasha na hadin gwiwa don bunkasa ci gaba
2017-07-25 13:13:42 cri

Kasar Habasha kasa ce da ta zama abin koyi a fannin hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka ta fuskar masana'antu, haka kuma tana daya daga cikin kasashen da suka fi samun muradu bisa shawarar "Ziri daya da hanya daya". A cikin shekaru 12 da suka gabata, kasar Sin ta riga ta zama abokiyar Habasha mafi girma a fannonin cinikayya, da gine-gine, da ma zuba jari. Sakamakon hadin gwiwa tare da kamfanonin kasar Sin, kasar Habasha ta samu saurin ci gaban masana'antu, da zamanintar da birane, da ma kyautatuwar zaman jama'arta.

A kasar Habasa da ke kuryar Afirka, akwai dimbin ayyuka irin su na farko da ke da nasaba da kasar Sin, kamar cibiyar raya masana'antu, da aikin samar da wutar lantarki bisa karfin iska, da hanyar motoci mafi sauri, da layin dogo cikin birane, gami da layin dogo na zamani a tsakanin kasa da kasa.

Bisa kididdigar da bankin duniya ya bayar, an ce, a cikin shekaru 12 da suka gabata, matsakaicin saurin karuwar GDP na Habasha ya zarce kashi 10 cikin 100, lamarin da ya sa kasar zama daya daga cikin kasashen da suka fi samun saurin ci gaban tattalin arziki a duniya. A waje daya kuma, a matsayinta na abokiyar Habasha mafi girma a fannonin cinikayya, da gine-gine, da ma zuba jari, kasar Sin ta ingiza bunkasuwar tattalin arzikin Habasha sosai.

A karshen watan jiya, an bude cibiyar raya masana'antu ta Hawassa a kasar Habasha, wadda ta kasance cibiyar raya masana'antu ta farko da gwamnatin kasar ta zuba jari a kai. Firaministan kasar Hailemariam Dessalegn ya bayyana cewa, sakamakon cibiyar, sha'anin masana'antun kasarsa ya bude wani sabon shafi. Ana saran ganin Habasha ta zama cibiyar sana'ar masana'antu ta nahiyar Afirka ya zuwa shekarar 2025.

A cikin dakunan masana'antu, ma'aikatan kasar Habasha na amfani da injuna yadda ya kamata, domin kera kayayyakin da za a fitar da su zuwa kasashen Turai da Amurka. A cikin wannan cibiyar raya masana'antu da fadinta ya kai kadada 130, za a iya samar da guraban aikin yi dubu 60, yawan kudin da za a samu daga fitar da kayayyaki zuwa ketare zai kai Dala biliyan daya a ko wace shekara.

Wannan cibiyar raya masana'antu da kamfanin CCECC na kasar Sin ya gina yake kuma kula da aikin gudanar da ita, an kafa wani sabon salo, wato gwamnatin Habasha ce ta zuba jari, kamfanin kasar Sin kuma ta kula da aikin gudanar da ita har na tsawon shekaru uku bayan da ta kammala aikin gina ta, sa'an nan za a yada irin salon ta a duk fadin kasar. Bisa fasahohin da aka samu daga wannan cibiyar, ana saran gina cibiyoyin raya masana'antu fiye da 10 a cikin shekaru da dama masu zuwa a kasar Habasha.

A ganin jama'ar kasar, cibiyar raya masana'antu wata alama ce ta zamanintar da kasarsu, wadda za ta sa kaimi ga ci gaban tattalin arzikin kasarsu. Bisa shirin na biyu da gwamnatin kasar Habasha ta bayar ta fuskar tattalin arziki, ya zuwa shekarar 2020, jimillar GDP da kasar za ta samu daga ribar masana'antun kere kere zai karu daga kaso 5 zuwa kaso 10 cikin 100, kana jimillar GDP da za ta samu daga fitar da kaya zuwa ketare ma za ta karu zuwa kashi 20 cikin dari.

A hannu guda za a mai da hankali wajen raya aikin sake-sake, da sarrafa fatu, da amfanin gona, da ma harhada kayan latironi, a kokarin shigar da kasar cikin kasashe masu matsakaicin kudaden shiga. Domin cimma wadannan bukata, gwamnatin Habasha ta tsara shirin raya cibiyoyin raya masana'antu.

Bisa labarin da aka samu, an ce, dukkan cibiyoyin raya masana'antu 8 da ake gina su yanzu, kamfanonin kasar Sin ne suka sa hannu a kai. A ciki, an riga an gudanar da wasu. Kamar a cikin masana'antar samar da takalmai ta Huajian, an dauki ma'aikata mazauna wurin fiye da 8000. Mr. Demissie, manaja na masana'antar Huajian ya gaya wa wakilinmu cewa, a bayan ko wane ma'aikaci, akwai wani gida. Ko wane gurbin aikin na alamanta kyautatuwar zaman rayuwar wani gida.

Ali Issa, shugaban zartaswa ne na cibiyar nazarin tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kuryar Afirka, ya kuma bayyana cewa, kasar Sin ta zabi Habasha, Habasha ita ma ta zabi kasar Sin. Ana fatan ganin karin ayyukan hadin kan kasashen biyu nan gaba, ganin yadda Habasha ta fara samun bunkasuwa ba da dadewa ba. A ganinsa, yunkurin ci gaban kasar Sin ya zama abin koyi ga Habasha.

Bayan da ta raya tattalin arzikinta har na tsawon shekaru fiye da 30, kasar Sin ta riga ta zama kasa mafi girma ta biyu a duniya ta fuskar tattalin arziki. Mr. Ali ya ce, Habasha tana son yin dukkan abubuwan da kasar Sin ta taba yi. Za ta koyi fasahohin kasar Sin a fannonin masana'antu, da aikin gona, da muhimman ayyukan ababen more rayuwa, sa'an nan ta hada su tare da yanayin da kasar take ciki, a kokarin kara samun bunkasuwa.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China