in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na ci gaba da kasancewa jigo na farfadowar tattalin arziki, in ji IMF
2017-07-25 09:23:26 cri

Babban masani kuma daraktan ofishin bincike da ba da shawara kan harkokin tattalin arziki na bankin ba da lamuni na IMF Maurice Obstfeld, ya ce Sin za ta ci gaba da kasancewa jigo a fannin farfadowa, da kuma bunkasar tattalin arzikin duniya.

Mr. Obstfeld wanda ya bayyana hakan, yayin wata zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua game da daidaita hasashen da IMF ya yi, bisa habakar tattalin arzikin kasar ta Sin na bana wanda ya daga zuwa kaso 6.7, da na shekara mai zuwa da zai kai kaso 6.4 bisa dari, ya kuma ce, ya zuwa yanzu an ga alamu dake nuni ga ci gaban da Sin ta samu sama da hasashen da IMF din ya yi a baya.

Jami'in ya kara da cewa, karuwar bunkasar tattalin arzikin kasar zuwa kaso 6.9 a watanni 3 na tsakiyar wannan shekara, ya dara abun da aka tsammata. Don haka dai ga dukkanin alamu, al'amuran tattalin arzikin Sin na garawa yadda ya kamata.

Har wa yau Mr. Obstfeld ya bayyana wannan ci gaba a matsayin wanda zai zaburar da tattalin arzikin sassan nahiyar Asiya, da ma daukacin sassan duniya baki daya, kasancewar Sin kasa da a ko da yaushe, ci gaban ta a wannan fanni ke da matukar tasiri ga sauran sassa na duniya.

An dai wallafa sabon hasashen na IMF a ranar Litinin, 'yan kwanaki bayan da Sin ta fidda alkaluma dake nuna tagomashi da tattalin arzikin na ta ke samu a watanni 3 na tsakiyar wannan shekara da muke ciki. Mahukuntan kasar kuma sun alakanta hakan da sauye sauye da ake gudanarwa a fannonin tattalin arzikin kasar, ciki hadda rage yawan hajoji sama da bukata da kamfanonin kasar ke fitarwa.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China