in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jagororin jam'iyyar APC a Najeriya sun ziyarci shugaban kasar dake jinya a Burtaniya
2017-07-25 09:10:58 cri

Wasu kusoshi na jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya a ranar Lahadi sun gana da shugaba Muhammad Buhari a birnin Landan na kasar Burtaniya inda yake jinya.

Mai magana da yawun shugaban Najeriyar Femi Adesina ya bayyana cikin wata sanarwa da ta iske kamfanin dillancin labarai na Xinhua a birnin Legas cewa, tawagar wakilan jam'iyyar ta APC sun hada da shugaban jam'iyyar na kasa John Odigie-Oyegun.

Kakakin shugaban kasar ya ce, shugaban yana cikin annushuwa da kuma halinsa na raha.

Adesina ya ambato gwamnan jihar Imo dake kudancin kasar Rochas Okorocha yana cewa, tawagar wakilan jam'iyyar sun shafe sama da sa'a guda suna cin abincin rana tare da shugaba Buhari, kuma wannan ya sha banban da irin maganganun da wasu ke yadawa a cikin kasar game da lafiyar shugaban na Najeriya.

A cewarsa, shugaban kasar ya yi matukar farin ciki da wannan ziyarar da suka kai masa, kana ya tambaye su gwamnonin game da halin da jihohinsu ke ciki.

Ya kara da cewa, shugaba Buhari ya tambayi ministan sufuri na kasar, Rotimi Ameachi, game da yadda ayyukan layin dogo ke gudanar a kasar.

A cewar Okorocha, abin da wasu ke yadawa game da lafiyar shugaba Buhari karairayi kawai.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China