in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministocin AL za su gana game da takaddamar Isra'ila da Palasdinawa
2017-07-24 14:07:48 cri

Ministocin harkokin wajen kungiyar kasashen Larabawa ta AL, za su gana game da takaddamar tsagin Isra'ila da Palasdinawa, game da masallacin Aqsa.

A kwanakin baya ne dai wasu Larabawa 3 suka harbe wasu 'yan sanda Yahudawa su biyu a kusa da masallacin na Aqsa, lamarin da ya sanya 'yan sandan Isra'ila hallaka 'yan bindigar tare da rufe masallacin. Kawo yanzu kuma ana ta ci gaba da samun dauki ba dadi tsakanin jami'an Isra'ila da Palasdinawa masu zanga zanga a harabar masallacin.

A ranar 14 ga watan nan na Yuli kuma jami'an tsaron Isra'ila suka sanya wasu na'urori na tantance ko masu shiga masallacin na Aqsa na dauke da karafa a jikin su, lamarin da ya dada tsananta yanayin da ake ciki a masallacin, da ma yankunan dake yamma da kogin Jordan.

Ko da a ranar Juma'a ma sai da sassan biyu suka yi taho mu gama, wanda hakan ya sabbaba rasuwar Palasdinawa 3 tare da raunata wasu da dama.

A cewar kakakin kungiyar kasashen Laraba ta AL Mahmoud Afifi, wakilan kungiyar za su gana ne a ranar Laraba bisa shawarar kasar Jordan, a helkwatar kungiyar dake birnin Alkahirar Masar. Tuni kuma kungiyar ta yi tofin-Ala-tsine game da matakan cusgunawa Palasdina da Isra'ila ke dauka a masallacin Aqsa, wanda hakan ya sabawa 'yancin masu bauta, da ma sauran dokoki na kasa da kasa da kudurorin da MDD ta gindaya.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China