in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabar Liberiya ta yabawa 'yan sandan kasar Sin masu tabbatar da zaman lafiya
2017-07-24 11:04:41 cri

Ranar 22 ga wata, shugaba Ellen Johnson-Sirleaf ta kasar Liberiya ta gabatar da wani jawabi, inda ta nuna godiya dangane da gudummowar da 'yan sandan kasar Sin masu aikin kiyaye zaman lafiya suke bayarwa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasarta, ta kuma godewa gwamnatin kasar Sin bisa goyon bayanta kan raya kasar ta Liberiya.

Madam Ellen Johnson-Sirleaf ta fadi haka ne a yayin bikin sake amfani da filin wasa na SKD na Liberiya, wanda kasar Sin ta taimaka wajen gina shi.

Shugabar Liberiya ta ce, a yayin da muke gamuwa da matsala, nan take kasar Sin ta bamu taimako. Akwai shaidu masu yawa da suka nuna cewa, jama'ar Sinawa abokanmu ne na gaskiya. Ina fatan Liberiya da Sin za su cigaba da yin hadin gwiwa, da kyautata dankon zumuncinmu, a kokarin raya huldar da ke tsakaninmu zuwa sabon matakai. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China