in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasuwar neman ayyuka a Sin ta inganta cikin rubu'i na 2 a bana
2017-07-24 09:43:55 cri

Wani bincike da cibiyar bincike kan guraben ayyukan yi ta jami'ar Renmin dake kasar Sin, da hadin gwiwar cibiyar CIER suka gudanar ya nuna cewa, kasuwar neman guraben ayyukan yi ta Sin na dada kyautata a rubu'i na biyu wato tsakanin Afililu da Yunin shekarar nan ta 2017.

Alkaluman kididdigar binciken sun nuna cewa, an samu kyautatuwar yanayin samun guraben ayyuka daga kaso 1.19 a watanni ukun farkon shekarar, ya zuwa kaso 2.26 a watanni ukun tsakiya.

Binciken ya bayyana cewa, wannan ci gaba da aka samu na da nasaba da karin guraben ayyukan yi da aka samu, sakamakon fadadar tattalin arziki, da raguwar yawan masu neman guraben aikin yi, alama dake nuna cewa, yanzu ba lokaci ne na yawan sauya ayyuka ba.

Har ila yau, alkaluman cibiyar CIER sun nuna cewa, sassan hada hadar cinikayya ta yanar gizo na kan gaba wajen bukatar al'umma, yayin da sassan makamashi, da na hakar ma'adanai ke kara samun ci gaba. Sai kuma fannin ba da hidimar kwararru a bangaren wasannin na'ura mai kwakwalwa, wanda ake matukar bukatar masu aiki a cikin ta, duba da irin dinbin riba da sashen ke samarwa.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China