in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mahukuntan Somaliya sun ja kunne cibiyoyin kudi game da tallafawa Al Shabaab
2017-07-24 09:33:23 cri

Mahukuntan kasar Somaliya, sun ja kunne kamfanonin sadarwa da sauran cibiyoyin musayar kudade, ciki hadda bankuna dake hada hada a kasar, da su kauracewa tallafawa kungiyar Al Shabaab wajen tura mata kudade.

Ana dai zargin wadannan sassa da turawa kungiyar ta 'yan ta'adda kudaden wadanda jama'a ke aikawa, ko dai a matsayin tallafi, ko kuma tara da take dorawa 'yan kasuwa da sauran al'ummun kasar.

Da yake tabbatar da hakan, ministan tsaron cikin gidan Somaliya Mohamed Islow, ya ce gwamnati ta kaddamar da wani kudurin doka ta musamman a ranar Asabar, wadda ta haramta tura kudade asusun kungiyar Al Shabaab.

A daya bangaren kuma, dokar ta ja kunne al'ummar kasar da su kauracewa biyan duk wata tara ga wannan kungiya, ko kuma su fuskanci fushin shari'a. Ministan ya ce, ko alama, gwamnati ba za ta saurari wani uzuri daga wadanda suka karya wannan doka ba.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China