in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta bada da umarnin kama jagoran Boko Haram a mace ko a raye
2017-07-23 13:04:07 cri

Babban hafsan sojojin Najeriya Laftanar Janar Tukur Buratai ya umarci dakarun sojin kasar da su damke babban madugun kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau, a mace ko a raye.

Cikin wata sanarwa da aka baiwa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a Lagos, birnin kasuwancin kasar, Buratai ya umarci manjo janar Ibrahim Attahiru, babban kwamandan rundunar wanzar da tsaro mai taken Lafiya Dole, dake Maiduguri, da ya kamo jagoran na Boko Haram cikin kwanaki 40.

Ya umarci kwamandan da ya baza jami'ansa dukkan yankuna da ake zaton maboya ce ta Shekau a duk fadin kasar.

Buratai ya bukaci al'umma da su tallafawa jami'an sojin kasar da dukkan muhimman bayanai da za su taimaka wajen kakkabe ayyukan mayakan 'yan ta'addan.

A watan Nuwambar shekarar 2016, rundunar sojin Najeriya ta ayyana neman jagoran kungiyar Boko Haram, tare da wasu mayakan kungiyar 54, a matsayin wadanda take nemansu ruwa a jallo, bisa zarginsu da jagorantar hare haren ta'addanci a sassan kasar.

Daukar wannan matakin, ya biyo bayan ikirarin da kakakin rundunar sojin Najeriya Sani Usman, ya yi ne watanni biyun da suka gabata, inda ya bayyana cewa, an jiwa Shekau munanan raunuka a lokacin da dakarun tsaron Najeriyar suka fatattaki 'ya'yan kungiyar Boko Haram daga dajin Sambisa wacce ke zama babbar maboya ga mayakan.

Sai dai Shekau ya sha musanta ikirarin da sojojin Najeriya suka sha yi na hallaka shi.

A watan Satumbar shekarar 2014, jami'an tsaron Najeriyar suka bada sanarwa cewa wani mai suna Mohammed Bashir, ya wallafa cewa a wani abu da ba'a saba ganin irinsa ba game da Shekau shi ne an dauke shi.

Sai dai rundunar sojin ta ce ta hallaka shugaban kungiyar a lokacin samamen da ta kai a dajin Sambisa.

Amma daga bisani Shekau ya yi watsi da rahoton hallaka shi kamar yadda aka fitar cikin wani faifan bidiyo 'yan kwanaki kadan bayan ikirarin sojojin.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China