in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jack Ma ya sanar da shirye-shiryensa hudu don tallafawa Afirka
2017-07-22 13:13:54 cri


A yayin taron koli kan inganta cudanya tsakanin matasan Afirka wanda aka yi a birnin Kigali na kasar Rwanda, wanda ya kafa hamshakin kamfanin cinikayya ta Intanet wato Alibaba a kasar Sin, Mista Jack Ma, ya sanar da shirye-shiryensa guda hudu, da zummar taimakawa mutanen Afirka.

Gwamnatin kasar Rwanda, da hadin gwiwar hukumar MDD ta bunkasa cinikayya da neman ci gaba(UNCTAD), da ta raya kasashe da kyautata rayuwar al'umma (UNDP) ne suka shirya taron kolin na matasan Afirka, inda ya samu halartar wakilai kusan dubu uku daga kasashe 90.

Mahalarta taron sun tattauna dangane da batutuwa da dama, ciki har da yadda za a inganta kwazon matasan nahiyar ta Afirka.

Hamshakin dan kasuwan kasar Sin, Jack Ma shi ma ya halarci taron, inda ya bayyana cewa:

"Na samu kwarin-gwiwa sosai a wadannan kwanaki a Afirka. Na yi imanin cewa, Afirka za ta bada babbar gudummawa ga ci gaban tattalin arzikin fadin duniya. Kuma a wannan nahiya, muna iya samun wasu dabaru da duniya take bukata, na habaka tattalin arziki. Don haka, zan sanar da shirye-shiryena guda hudu."

Shirinsa na farko shi ne, kamfaninsa wato Alibaba, zai hada-gwiwa da hukumar bunkasa cinikayya da neman ci gaba ta MDD, domin gayyatar matasan Afirka dari biyu su je birnin Hangzhou na kasar Sin, inda za su nakalci dabarun da suka shafi yin cinikayya ta kafar Intanet da makamantansu.

Jack Ma ya kara da cewa:

"Za mu himmatu wajen horas da wadannan matasan Afirka. Bayan sun gama karatu a kasar Sin, za su iya komawa yankunansu, inda za su iya raya sana'o'i da kansu, tare da taimakawa karin mutanen nahiyar."

A shirinsa na biyu, Jack Ma zai karfafa hadin-gwiwa da hukumomin kasashen Afirka daban-daban, domin kara horas da mutanen nahiyar a fannin Intanet.

Game da shirinsa na uku, Jack Ma ya bayyana cewa, zai kafa wani asusu, na bada kyautar kudi ga mutane masu aikin sintiri domin kiyaye gandun daji a kasashen Afirka.

Shirinsa na hudu, wato shiri na karshe shi ne, zuba jari domin baiwa matasan Afirka kwarin-gwiwar habaka sana'o'insu, Ma yana mai cewa:

"Ina so in nuna irin tabbacin da nake da shi a kanku, wato zan ware wani asusu na musamman na dala miliyan goma don taimakawa matasan Afirka raya sana'o'insu, a kokarina na tallafawa matasan cimma burinsu."(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China