in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
APU ta kammala taron kwamitin zartarwarta a Morocco
2017-07-22 12:09:41 cri
An kammala taro karo na 70 na kwamitin zartarwa na Tarayyar majalisun dokokin Afrika APU, jiya Juma'a a birnin Rabat na kasar Morocco.

Taron na yini biyu, ya mai da hankali ne kan inganta hadin gwiwa tsakanin majalisun dokokin kasashen Afrika.

Shugaban kwamitin Cipriano Cassama, ya ce taron ya bada damar tattauna kalubale daban-daban da kasashen Afrika ke fuskanta, ciki har da ta'addanci da rashin aikin yi da fatara. Inda ya jaddada cewa, shawo kan wadanan kalubale na bukatar karin musayar ra'ayi tsakanin mambobin majalisun dokokin kasashen nahiyar. Kwamitin ya yanke shawarar gudanar da taronsa na 71 a Burkina Faso daga ranar 6 zuwa 10 ga watan Nuwamban bana.

APU Kungiya ce da ta kunshi majalisun dokokin kasashen nahiyar Afrika, wadda aka kafa a watan Fabrerun 1976 a birnin Abidjan na kasar Ivory Coast. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China