in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mukaddashin shugaban Nijeriya ya ba da umarnin ceto wasu mata da aka sace
2017-07-21 09:16:00 cri

Mukaddashin shugaban kasar Nijeriya Yemi Osinbajo, ya umarci shugabannin hukumomin tsaro na kasar su tabbatar da ceto wasu mata da ake zargin mayakan Boko Haram sun sace a baya-bayan nan a jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar.

Yemi Osinbajo, ya kuma yi tir da sace matan, yana mai bayyana al'amarin a matsayin mugunta.

Cikin wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu jiya Alhamis a Lagos, cibiyar hada-hadar kasuwanci ta kasar, mukaddashin shugaban kasar wanda ya jajantawa iyalan matan, ya ba da tabbacin cewa, gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba, wajen tabbatar da gaggauta ceton su lami lafiya.

Yemi Osinbajo, ya umarci rundunar sojin kasar da hukumomin tsaro na farin kaya su dauki dukkan matakan da suka dace, ciki har da hada hannu da takwarorinsu na kasashen waje domin ceto matan.

Har ila yau, ya bukaci su tabbatar da karfafa harkokin tsaro a ciki da wajen jihar Borno. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China