in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhun MDD ya yi taron muhawara kan zaman lafiya a Afirka
2017-07-20 10:59:32 cri

Jiya Laraba kwamitin sulhun MDD ya shirya wani taron muhawara a bainar jama'a karkashin jagorancin kasar Sin wadda ke rike da shugabancin karba karba na kwamitin na wannan wata, domin tattauna batutuwan da suka shafi wanzar da zaman lafiya da tabbatar da tsaro a nahiyar Afirka.

An shirya wannan taro ne domin sa kaimi ga kasashen duniya su kara samar da goyon baya ga kasashen Afirka wajen kara karfafa aikin wanzar da zaman lafiya da kuma tabbatar da tsaro a nahiyar Afirka baki daya. Babban sakataren MDD Antonio Guterres da kwamishinan kungiyar tarayyar kasashen Afirka AU mai kula da harkokin zaman lafiya da tsaro Smail Chergui da sauran manyan jami'ai ne suka halarci taron.

Zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Liu Jieyi ya bayyana a yayin taron cewa, kokarin da kwamitin sulhun MDD yake yi domin jawo hankalin kasashen duniya da su kara samar da goyon baya ga kasashen Afirka, musamman ma wajen tabbatar da zaman lafiya da kuma tsaro, zai kara ciyar da zaman lafiya da tsaro gaba a duk fadin duniya. Yana mai cewa, "Batun zaman lafiya da tsaro batu ne da ya sha dukkan yankunan kasa da kasa, don haka tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Afirka ya shafi muradun al'ummomin kasashen duniya baki daya, saboda haka hakki ne mai muhimmanci na kwamitin sulhun MDD."

A jawabinsa babban sakataren MDD Antonio Guterres ya nuna yabo da godiya ga kasar Sin da taron muhawara na bainar jama'a game da shimfida zaman lafiya da tsaro a nahiyar Afirka da ta kira. Guterres ya bayyana cewa, "Ina da imani cewa, kasashen duniya za su canja ra'ayin nuna bambanci ga nahiyar Afirka, da amincewa nahiyar Afirka tana da makomar bunkasuwar tattalin arziki, da kafa dandalin hadin gwiwa bisa wannan tushe. A fannin kiyaye tsaro, kungiyar AU da MDD suna daukar matakai don inganta tsarin magance barkewar rikici, suna kuma kokarin kawar da barazana kafin rikici ya tsananta, tare da inganta karfin tinkarar rikice-rikice. Kasashen duniya suna fuskantar kalubale a fannin kiyaye zaman lafiya da tsaro yayin da ake kokarin kara karfin nahiyar Afirka a wannan fanni, don haka yana da muhimmanci sosai a inganta karfin nahiyar Afirka a wannan fanni."

Jami'in kungiyar AU mai kula da harkokin kiyaye zaman lafiya da tsaro Smail Chergui ya yi godiya ga kwamitin sulhun MDD bisa ga taron muhawara da ya shirya a bainar jama'a game da batun zaman lafiya da tsaro na Afirka a karkashin jagorancin shugabar kwamitin sulhu na wannan karo wato kasar Sin, kana ya nuna yabo ga MDD bisa ga raya dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakaninta da kungiyar AU.

A yayin taron muhawarar, Mista Liu Jieyi ya kuma yi nuni da cewa, "Har kullum kasar Sin na tsayawa tsayin daka kan mara wa kasashen Afirka baya da su warware batutuwansu da kansu kuma ta hanyar da ta dace da su. Kasar Sin ta shiga ayyukan kiyaye zaman lafiya da MDD take gudanarwa a kasashen Afirka cikin himma da kwazo. Yanzu haka akwai sojojin kasar Sin masu aiki kiyaye zaman lafiya fiye da 2600 dake gudanar da ayyukansu a kasashen Afirka. Ban da haka kuma, kasar Sin ta shiga ayyukan yaki da 'yan fashin teku da ba da kariya ga zirga-zirgar jiragen ruwa a yankin tekun Somaliya. A shekarar 2015 da ta gabata, a yayin taron dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin kasashen Sin da Afirka, kasar Sin ta kaddamar da manyan shirye-shiryen hadin gwiwa guda 10 a tsakanin kasashen Sin da Afirka, wadanda suka shafi bunkasuwa, rayuwar al'umma, zaman lafiya da tsaro da dai sauransu. A dangane da batun wanzar da zaman lafiya da tsaro kuwa, kasar Sin tana himmantuwa wajen inganta karfin kasashen Afirka na kiyaye zaman lafiya da kansu. Yanzu ana gudanar da ayyukan masu ruwa da tsaki. Shawarar ziri daya da hanya daya da kasar Sin ta gabatar, tana iya taimakawa kasashen Afirka wajen samun ci gaba, ta yadda za su iya warware rikicin dake addabarsu baki daya. Kasar Sin za ta inganta hadin gwiwa a tsakaninta da kasashen Afirka bisa shawarar ziri daya da hanya daya, za kuma ta ci gaba da ba da taimako da goyon baya ga kasashen Afirka wajen inganta karfinsu na kiyaye zaman lafiya da tsaro, a kokarin warware rikice-rikicen shiyya-shiyya cikin hanzari da kuma tabbatar da samun zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaba a nahiyar ta Afirka cikin sauri.(Jamila Tasallah Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China