in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta girke jiragen ruwan yaki a gabar tekun Guinea don fatattakar masu fashin jirgin ruwa
2017-07-20 09:05:38 cri

Rundunar sojin ruwa ta Najeriya ta sanar da cewa, an tura jiragen ruwan yaki da sojojin ruwa a wani babban aikin sintiri da dakarun ruwan kasar ke yi domin kawo karshen masu fashin teku dake afkawa manyan 'yan kasuwa na cikin gida da na kasa da kasa a gabar tekun Guinea.

Shirin sintirin ya kunshi kakkabe dukkan manyan barayi dake kaddamar da hare hare kan muhimman kayayyakin hakar albarkatun mai da iskar gas na kasar, da kawar da sauran bata gari a gabar tekunan kasar, kamar yadda babban jami'in sojin ruwan na Najeriya Iboke-Ete Ibas ya tabbatar da hakan.

Ya bayyana hakan ne a wajen kaddamar da shirin mai taken "Tsare Teku V" a yankin Onne na jihar Rivers.

Wannan shirin dai ci gaba ne daga shirin da aka kaddamar a watanni 3 na farkon shekarar 2016, domin kare kayayyakin samar da albarkatun mai da iskar gas na kasar, da lura da sauran batutuwan tattalin arziki.

A cewarsa, aikin sintirin ya haifar da kyakkyawan sakamako da kuma inganci a fannin kiyaye lafiyar jiragen ruwa da bangaren kula da kayayyakin ayyukan samar da mai da iskar gas na kasar.

Ya ce, an samu nasarori masu yawa idan aka kwatanta da cewa, hare hare 4 ne kawai aka fuskanta tsakanin watan Janairun zuwa Yuni na 2017, yayin da tsakanin watan Janairun zuwa Yunin na shekarar 2016, an samu irin wadannan hare hare har guda 36.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China