in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi ya yi shawarwari da takwaransa na Palasdinu
2017-07-19 11:10:59 cri

A jiya Talata ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi shawarwari da shugaban Palasdinawa Mahmoud Abbas, wanda ke yin ziyara a nan birnin Beijing, inda shugaba Xi ya gabatar da shawarwari guda hudu kan yadda za a daidaita batun Palasdinu yadda ya kamata.

Yayin ganawarsu, shugaba Xi Jinping ya gabatar da shawarwari hudu kan yadda za a daidaita batun Palasdinu, kuma ya jaddada cewa, kasar Sin za ta ci gaba da bada taimako domin daidaita batun Palasdinu ta hanyar siyasa kamar yadda ta yi a baya, shugaba Abbas shi ma ya amince da shawarwarin da shugaba Xi ya gabatar. Shugabannin biyu sun kuma bayyana cewa, za su hada kai tare domin ciyar da hadin gwiwar sada zumunta dake tsakanin Sin da Palasdinu gaba.

Shugaba Xi ya darajanta zumuncin dake tsakanin kasashen biyu matuka, yana mai cewa, "Mu Sinawa mu kan bayyana cewa, tsohuwar aminiya kamar zinariya take, saboda zumuncin dake tsakaninsu ba zai sauya ba har abada, tun tuni kasar Sin tana goyon bayan kasar Palasdinu, a cikin shekaru sama da hamsin da suka gabata, al'ummomin kasashen biyu suna nunawa juna goyon baya bisa tushen fahimtar juna, hakika su 'yan uwa ne."

Shugaba Xi ya ci gaba da cewa, kasar Sin tana fatan za ta ci gaba da gudanar da hadin gwiwa dake tsakaninta da kasar Palestinu, musamman ma wajen aiwatar da shawarar ziri daya da hanya daya, da gina yankin masana'antu, da aikin horas da kwararrun jami'ai, da gina tashar samar da makamashin hasken rana da sauransu, domin kara ci gaban Palasdinu.

Shugaba Abbas ya amince da hakan, ya ce, "Ina son in nuna godiya ga shugaba Xi Jinping saboda ganawar da ya yi da ni a nan birnin Beijing, wannan shi ne karo na hudu da na kawo ziyarar aiki kasar Sin a matsayina na shugaban Palasdinwa, kuma a cikin shekarun da suka gabata, na sha zuwa kasar Sin, yau shi ne karo na biyu da na yi ganawa da shugaba Xi, a baya, na taba ganawa da wakilan tawagoyin da gwamnatin kasar Sin ta tura zuwa Palasdinu, ina ganin cewa, ziyarar dake tsakanin sassan biyu ta kara zurfafa dadadden zumuncin dake tsakaninmu."

Game da yadda za a kokarin da ake yi domin daidaita batun Palasdinu, shugaba Xi ya gabatar da shawarwari, inda ya bayyana cewa, ya kamata a ci gaba da sanya kokari domin daidaita batun ta hanyar siyasa bisa tushen aiwatar da shirin kafa kasashe biyu.

Bayan ganawar shugabannin kasashen biyu, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Zhang Ming ya yi bayyani kan shawarwarin da kasar Sin ta gabatar ga manema labarai, ya ce, "Kasar Sin ta nace ga shirin kafa kasashe biyu, kuma tana goyon bayan a kafa kasar Palasdinu mai 'yancin kai bisa tushen amincewa da iyakar kasa da aka shata a shekarar 1967, kana gabashin birnin Kudus a matsayin hedkwata, kuma ta yi kira ga bangarorin da abin ya shafa da su aiwatar da kudurin kwamitin sulhun MDD mai lamba 2334, su daina gina matsuguni a yankin da suka mamaye nan take, kana su daina kai hari ga fararen hula, tare kuma da maido da shawarwari cikin hanzari. Ban da haka kuma, kamata ya yi kasashen duniya su kara sulhuntawa tare kuma da daukar matakan shimfida zaman lafiya, ta yadda za a daidaita batun ta hanyar siyasa lami lafiya. Har kullum kasar Sin tana mayar da Palasdinu da kuma Isra'ila muhimman abokai yayin da ake aiwatar da shawarar ziri daya da hanya daya, kana tana fatan za a gudanar da shawarwari tsakanin sassan uku wato Sin da Palestinu da kuma Isra'ila domin gudanar da hadin gwiwar moriyar juna."

Bayan shawarwarin, shugaba Abbas ya mika wa shugaba Xi lambar yabo ta matsayin koli ta kasar Palasdinu, domin nuna godiya ga kasar Sin saboda goyon bayan da take baiwa Palasdinu cikin adalci, tare kuma da nuna girmamawa ga shugaba Xi, game da wannan, shugaba Xi shi ma ya nuna godiyarsa, yana mai cewa, "Ba ni kadai aka baiwa wannan lambar yabo ba, lambar yaba ce da aka da ka baiwa kasar Sin saboda matsayin adalcin da kasar Sin take nunawa kan batun Palasdinu. Kasar Sin ta nuna cewa, Palasdinu tana mai da hankali matuka kan huldar dake tsakaninta da kasar Sin. Duk da manyan sauye-sauye da yanayin duniya ke fuskanta, amma har kullum kasar Sin za ta ci gaba da goyon bayan sha'anin adalci na al'ummar Palasdinu, haka kuma za ta ci gaba da yin kokari domin ciyar da huldar dake tsakanin sassan biyu gaba."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China