in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fara shawarwari zagaye na biyu game da shirin Birtaniya na ficewa daga EU
2017-07-18 12:09:21 cri

A jiya ne, aka fara shawarwari zagaye na biyu game da shirin ficewar Birtaniya daga kungiyar EU. Michel Barnier, wakilin farko na kungiyar tarayyar Turai EU game da batun ficewar Birtaniya daga EU ya bayyana a wancan rana, cewar shawarwarin za su mai da hankali ne kan 'yancin 'yan kasashe mambobin EU da ke zaune a Birtaniya, da biyan kudin ficewar kasar daga kungiyar, da ma batun yankin arewacin Ireland. An yi hasashen cewa, akwai fargaba a shawarwarin saboda babban sabanin dake tsakanin EU da Birtaniya kan wadannan batutuwa.

A jiya Litinin ne, aka fara yin shawarwari zagaye na biyu kan shirin Birtaniya na ficewa daga EU a babbar hedkwatar hukumar kula da harkokin EU da ke Brussels. Ajandar da EU ta bayar, na nuna cewa, za a shafe kwanaki hudu ana gudanar da shawarwarin, wato za a kammala shi a ranar 20 ga wata. Kafin fara shawarwarin, sai da Mr. Barnier, wakilin farko na EU kan batun janyewar Birtaniya daga kungiyar da David Davis, ministan kula da ficewar Burtaniya daga EU suka gana da 'yan jarida, inda Mr. Barnier ya ce, yana da fata mai kyau a wannan shawarwarin. Yana mai cewa,

"Shawarwarin na wannan mako zai mai da hankali ne kan wasu muhimman batutuwa, za mu duba tare da kwatanta matsayin da bangarorin biyu ke dauka, a kokarin samun ci gaba. Kamar yadda kuka sani, za mu tattauna kan batutuwan da suka shafi 'yancin jama'ar kasashe mambobin EU da ke Birtaniya, da biyan kudin ficewa ga EU, da dai sauraunsu. Masu shiga tsakani kuwa za su tattauna kan batun Ireland a siyasance, a karkashin tanade-tanaden yarjejeniyar Lisbon."

A nasa bangaren kuma, Mr. Davis ya bayyana cewa, a watan jiya ne aka kaddamar da shawarwarin ficewar Birtaniya daga EU, kuma yanzu ana cikin wani muhimmin mataki na shawarwarin. Ya kara da cewa,

"Abin da ya fi muhimmanci gare mu shi ne samun ci gaban shawarwarin. Za mu tabbatar da sabanin da ke tsakanin bangarorinmu biyu cikin shawarwarin, da kuma yin kokarin daidaita shi. A waje daya kuma za mu tabbatar da matsaya daya da muke da su domin samun daidaito. Yanzu lokaci ya yi na kaddamar da aikinmu, kuma za mu yi kokarin ganin mun samu nasara."

Ko da yake EU da Birtaniya na ganin cewa, an shiga muhimmin mataki na shawarwarin, amma akwai babban sabani a tsakanin bangarorin biyu kan wasu muhimman batutuwa. a game da batun 'yancin jama'ar kasashe mambobin EU da ke Birtaniya, EU na fatan jama'a miliyan 3.2 'yan kasashe mambobin EU da ke zauna a Birtaniya za su samun hakkinsu kamar da, amma bisa shirin da Birtaniya ta gabatar, an kayyade hakkin da wadannan mutane za su samu a fannonin samun iznin zama a kasar, da haduwa da iyalansu, da dai sauransu. Ko da yake EU ta sha nuna rashin jin dadinta kan wannan shirin, amma sakataren harkokin wajen kasar Birtaniya Boris Johnson da ke halartar taron ministocin harkokin wajen kasashe mambobin kungiyar EU a Brussels ya furta jiya cewa, shirin da kasarsa ta gabatar kan hakkin 'yan kasashe mambobin EU da ke Birtaniya na da adalci. Yana mai cewa,

"Shirin da gwamnatin kasar Birtaniya ta gabatar game da hakkin 'yan kasashe mambobin EU da ke kasar na da adalci sosai. Wannan wani shiri da kimanin jama'a miliyan 3.2 'yan kasashe mabobin EU da ke Birtaniya za su amfana da shi, za mu ba su tabbaci kan zamansu a nan gaba."

Batun biya kudin ficewa ga EU shi ma wata babbar matsala ce da ke ci wa kasar tuwo a kwarya. Ko da yake har yanzu ba a san yawan kudin ba, amma Jean Juncker ya taba bayyana cewa, yawan kudin zai kai kimanin EURO biliyan 60. Mr. Barnier ya furta a kwanan baya cewa, dole ne Birtaniya ta biya wadannan kudade. Amma sakataren harkokin wajen kasar Birtaniya Mr. Johnson ya mayar da martani cewa, EU ta bukaci kudin ficewa fiya da kima ne domin yi wa Birtaniya sharri, kasarsa ba za ta amincewa da wannan ba.

Saboda haka, ana ganin cewa, za a fuskanci matsala sosai yayin shawarwari na wannan zagaye. Ana kuma hasashen cewa, da kyar a iya samun daidaito kan muhimman batutuwa a shawarwarin.(Kande)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China