in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Nijeriya ta na da muradin inganta bangaren Kirkire-kirkire
2017-07-18 11:16:45 cri
Gwamnatin Nijeriya ta ce tana da muradin inganta bangaren kirkire-kirkire tare da saukaka haraji ga masu zuba jari a bangaren.

Mukadashin Shugaban kasar Yemi Osinbajo ne ya bayyana haka a jiya, lokacin bude taron yini biyu kan bangaren kirkire-kirkire a Lagos cibiyar hada-hadar kasuwanci ta kasar.

Yemi Osinbajo wanda ya bayyana bangaren a matsayin muhimmi ga tattalin arziki, ya ce bangaren na ba da gudumuwar kashi 1.45 ga alkaluman GDP kuma yana samun riba daga kayayyakin da yake fitarwa baya ga dimbin aikin yi da yake samarwa ga miliyoyin jama'a.

Mukkadashin shugaban kasar ya shaidawa mahalarta taron cewa, gudummuwar da bangaren ke badawa ga alkaluman GDP abun burgewa ne, idan aka kwatanta da kashi 11 da ake samu daga bangaren man fetur.

Ya ce la'akari da cewa gwamnati ba ta zuba jari a bangaren kamar yadda ta zuba a sauran bangarori ba, gudummuwar da bangaren ke bayarwa abu ne mai muhimmanci.

Yemi Osinbajo ya ce bisa karfafa gwiwar bangaren, gwamnati za ta kara karfin kudin shigar bangaren ta yadda zai rika samun riba tare kuma da saukaka kudin haraji ga masu zuba jari. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China