in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Boko Haram ta canza salon kai hare-hare a Nijeriya
2017-07-18 10:04:30 cri
Rundunar sojin Nijeriya ta ce kungiyar Boko Haram ta canza salon aiwatar da muggan ayyukanta a kasar.

Wannan na zuwa ne sa'o'i kalilan bayan mutane 12 sun mutu yayin da wasu 18 suka jikkata, sanadiyyar wasu hare-haren kunar bakin wake da aka kai Maiduguri, babban birnin Jihar Borno dake yankin arewa maso gabashin kasar.

Wata Sanarwa da kakakin rundunar sojin Onyema Nwachukwu ya fitar jiya a Lagos cibiyar hada-hadar kasuwanci ta kasar, ta ce 'yan tada kayar bayan na amfani da wasu sabbin dabaru na jan hankalin wadanda suke son kaiwa hari.

Onyema Nwachukwu ya kuma gargadi jama'a da su kula da sabbin dabarun 'yan tada kayar bayan, wadanda ke amfani da yara wajen kai harin kunar bakin wake.

Ya kara da cewa, 'yan tada kayar bayan sun dauki wata sabuwar dabara ta yaudara, domin samun mutane da dama da hari zai rutsa da su.

Kakakin rundunar sojin ya kuma shawarci al'umma da su mai da hankali tare da kauracewa duk wani taro da ba shi da muhimmanci domin yana iya jefa su cikin hatsari.

Har ila yau, ya yi kira ga iyaye su rika kula da zirga-zirgar 'ya'yansu domin kare su daga fadawa hannu 'yan ta'adda da ka iya amfani da su wajen aiwatar da muggan nufinsu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China