in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta bullo da tsarin hidimomin cinikayyar yanar gizo na bai daya
2017-07-17 10:50:33 cri

Ministan shari'a na kasar Sin Zhang Jun ya bayyana cewa, kasar Sin za ta bullo da wani tsarin samar da hidimomi na shari'a game da cinikayya ta yanar gizo ko kuma "One Stop" a Turance.

Zhang wanda ya bayyana hakan yayin taron karawa juna sani da ya gudana a Harbin dake lardin Heilongjiang a arewa maso gabashin kasar Sin, ya ce tsarin zai samar da wata kafa ta tuntubar juna bisa doka, da warware duk wata takaddama, samar da hidimar shari'a ga wadanda ke bukatar hakan, da kuma samun hidimar shari'a mai sarkakiya.

Ministan ya ce, karkashin wannan tsarin, kwararrun lauyoyi da ma'aikatan shari'a da doka ta amince da masu tantance alkalai ne kadai za su rika amsa tambayoyi a madadin hukumomi. A saboda haka, ministan Zhang ya yi kira ga jama'a da su rika amfani da fasahohin zamani irinsu "Internet plus" da manhajar Wechat, ta yadda jama'a za su ci gajiyar tsarin cikin sauki.

Tun a shekarar 1994 ne kasar Sin ta fara yunkurin kafa tsarin samar da hidimar shari'a ga jama'a, kuma daga lokacin zuwa shekarar 2013, sama da mutane miliyan 28 ne suka ci gajiyar wannan hidima, baya ga masu bukatar wannan hidima sama da miliyan biyar da aka karba.

Taron na Harbin dai ya samu halartar shugabannin sassan shari'a daga larduna daban-daban dake fadin kasar.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China