in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Trump ya karyata sakamakon kuri'ar jin ra'ayin jama'a game da farin jininsa
2017-07-17 10:02:41 cri

Wasu alkaluman kuri'ar jin ra'ayin jama'a da aka fitar a jiya Lahadi, na nuna cewa, farin jinin shugaba Trump na Amurka wanda ke dosar watanni shida a kan karagar mulki, kaso 36 cikin 100 ne kawai, adadi mafi kankanta da ba a taba samu ba cikin magabatansa a shekaru 70.

Sakamakon kuri'ar jin ra'ayin jama'ar wanda kafar watsa labarai ta ABC da jaridar Washington Post suka wallafa, na zuwa ne yayin tasirin Amurka ke kara raguwa a duniya, da jinkirin jam'iyyar Republican na aiwatar da manufofi, da kuma rahotanni dake ta wadari game da zargin kasar Rasha da hannu a yakin neman zaben Trump na shekarar 2016.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China