Da safiyar ranar Lahadi aka fara kada kuri'u a zaben majalisun dokokin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo da wasu kananan zabuka a kasar, sai dai wasu gundumomi 8 na kasar da ake fama da rashin cikakken tsaro wanda mayakan 'yan tawayen ninja suka haddasa, zaben bai gudana ba a wadannan yankuna.
A rumfuna zaben brazzaville, babban birnin kasar, akwai dar dar da ake da shi a sashen arewacin birnin, sai dai an ga cincirundon masu zaben a kudanci inda can ne babbar tungar kungiyoyin 'yan adawar kasar.
Zabukan biyu, ana sa ran mutane sama da miliyan 2 ne za su kada kuri'unsu domin sake zabar mambobin majalisar dokokin kasar su 151, da kuma shugabannin kananan yankunan kasar.
Shugaban tawagar sa ido a zaben daga kungiyar tarayyar Afrika AU, django cissoko, wanda tsohon firaministan kasar Mali ne, ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, zaben yana gudana, duk da jinkirin fara zaben a kan lokaci da aka samu a wasu wuraren.(Ahmad Fagam)