in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin tana adawa da dukkan aikace-aikacen da Dalai Lama ya yi wajen kawo barazana ga dunkulewar kasa
2017-07-15 13:30:48 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya ce Dalai Lama na 14, kan aiwatar da harkokin da suke haddasa rabuwar kasar Sin, kuma aniyarsa ita ce, raba yankin kabilar Zang wato Tibet daga kasar Sin.

A don haka, Gwamantin kasar Sin ta na adawa da dukkan aikace-aikacen da ya ke yi a kasashen ketare, wadanda za su haddasa rabuwar kasar, haka kuma, gwamnatin na adawa da dukkan jami'an kasashen ketare da ke shawarwari da kuma ganawa da Dalai Lama na 14.

A yayin taron manema labaran da aka yi jiya, 'yan jarida sun yi tambayoyi game da ra'ayin kasar Sin kan labarin da ofishin shugaban kasar Botswana ya fidda, wanda ke cewa Dalai Lama zai kai ziyara kasar cikin watan Agusta mai zuwa, inda shugaban kasar zai gana da shi, Sannan kuma, ko ziyarar Dalai Lama za ta yi illa ga ayyukan zuba jari da kamfanonin kasar Sin za su yi a kasar ta Botswana.

Dangane da wadannan tambayoyi, Geng Shuang ya jaddada cewa, kasar Sin tana tsayawa tsayin daka kan adawa da dukkan aikace-aikacen da Dalai Lama ya ke yi domin kawo rabuwar kasar, kuma ta na fatan kasashen da abin ya shafa za su girmama matsayin kasar Sin, yayin da tsai da kuduri kan batutuwan da abin ya shafa. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China