Abbas ya ce, gina matsugunan Yahudawa da Isra'ila ke yi, tare kuma da dokar da majalisar dokokin Isra'ila ta zartas wadda ita ce ta bada izinin kafa matsugunan Yahudawa a yammacin gabar kogin Jordan, dukkansu sun kawo illa ga kokarin da shugaban Amurka Donald Trump ya yi na farfado da zaman lafiya tsakanin Palasdinu da Isra'ila.
A nasa bangare sakatare-janar na kwamitin zartaswa na kungiyar 'yantar da Palasdinawa Saeb Erekat, ya fidda wata sanarwa a shekaran jiya, inda ya ce Palasdinu na fatan Amurka za ta iya tsara wani shiri, na kawo karshen mamayar da Isra'ila ta yi, da kafa wata 'yantacciyar kasar Palasdinu mai hedkwata a gabashin Kudus.(Murtala Zhang)