in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kudurin doka da zai warware dokokin da suka hade Birtaniya da EU na daf da bayyana
2017-07-14 10:20:31 cri

Babban jami'i mai lura da ficewar kasar Birtaniya daga tarayyar Turai David Davis, ya wallafa kudirin doka da zai baiwa kasar cikakkiyar damar yin sallama da kokokin kungiyar EU, wadanda suka hade kungiyar da Birtaniya.

Sai dai kudurin na shan suka daga jam'iyyun adawar kasar, wadanda ke ganin ko shakka babu zai fuskanci tirjiya, a zauren majalissar dokokin kasar.

Shi dai wannan kudurin doka, na da burin ganin Birtaniya ta cimma nasarar ficewa kaco kan daga tarayyar Turai nan da shekaru 2 masu zuwa, ba tare da fuskantar wani dabaibayi ba.

Kudurin dokar da Mr. Davis zai gabatar dai na cewa, dokokin kungiyar tarayyar Turai wadda a shekarar 1973 ta horewa Birtaniya damar shiga kungiyar ta EU, za su daina aiki kan Birtaniyar a ranar karshe da aka kammala shirin ficewar kasar daga EU.

Kaza lika kudurin zai magance tarnaki na dubban dokokin da suka hade Birtaniyar da kungiyar EU, matakin da a cewar Davis, shi ne hanya daya tilo, ta raba tafiyar sassan biyu salun alun, tare da tabbatar da cewa, a nan gaba, ba a fuskanci wasu matsaloli ba tsakanin sassan.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China