Li ya ce, akwai dadadden zumunci tsakanin kasar Sin da Equatorial Guinea. Yana fatan kasashen biyu za su kara samun fahimtar juna ta fuskar siyasa, da karfafa hadin-gwiwa, da mu'amala a fannonin da suka shafi zuba jari, da ayyukan gona, da harkokin yawon shakatawa, da al'adu da sauransu.
A nasa bangaren, Mista Mangue ya ce, kasarsa wato Equatorial Guinea na maida kasar Sin a matsayin wata kyakkyawar aminiya, kuma yana fatan dangantakar kasashen biyu za ta ci gaba da inganta a nan gaba.(Murtala Zhang)