in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in kungiyar OPEC ya bayyana fatan raguwar yawan mai da ake fitarwa kasuwa
2017-07-13 09:34:00 cri
Babban sakataren kungiyar kasashen masu fitar da danyen mai OPEC Mohammed Barkindo, ya ce yana da karfin gwiwar cewa yawan man da ake fitarwa a kasuwannin duniya zai ragu, ta yadda hakan zai daga darajar sa cikin watanni 6 na karshen wannan shekara ta bana.

Barkindo ya ce shekarar bana ta zo da tarin kalubale, sai dai duk da haka sannu a hankali kungiyar na cimma nasarori, a fannin yarjejeniyar da mambobin ta suka cimma, a babban taro game da man fetur karo na 22 da ya gudana a birnin Istanbul.

Cikin kalubalen da aka fuskanta a cewar sa, hadda batun karuwar yawan mai da kasashe wadanda ba mambobin kungiyar ta OPEC ne ba ke fitarwa, kamar Amurka wadda ke fitar da nau'in danyen mai da ake fitarwa daga duwatsu.

Daga nan sai Barkindo ya bayyana kudurin OPEC, na aiwatar da yarjejeniyar da suka kulla a bara tsakanin kasashe mambobin OPEC, da wadanda ba sa cikin ta, game da rage yawan danyen man da ake fitarwa da kusan ganga miliyan 1.2, kwatankwacin ganga 558,000 ke nan a ko wacce rana, da nufin daga darajar man a kasuwa.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China