in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar Boko Haram na ci gaba da kai hare-hare a Nijeriya
2017-07-13 09:14:55 cri
A baya-bayan nan, birnin Maiduguri, ya fuskanci jerin hare-hare, ciki har da wanda aka kai jami'ar birnin inda gomman mutane suka rasa rayukansu, ciki har da wani shehun malami.

A watan da ya gabata, hare-haren bomabomai sun kawo cikas ga bukukuwan karamar sallah a Maiduguri, birni mafi girma a yankin arewa maso gabashin Nijeriya.

A jiya Laraba ne rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar da mutuwar mutane 19 sanadiyyar wasu munanan hare-haren da aka kai birnin na Maiduguri a ranar Talata.

A cewar Kwamishinan 'yan sandan Jihar Borno Damian Chukwu, harin da ya auku ranar Talata da daddare, ya yi sanadin mutuwar jami'an tsaro na sa kai wato Civilian JTF guda 12 da fararen hula 7.

Damian Chukwu, ya shaidawa manema labarai a Maiduguri cewa, akalla mutane 23 ne suka jikkata sanadiyyar harin.

Wadannan hare-hare na zuwa ne kasa da sa'o'i 24, bayan babban hafsan sojin kasar Lt_Gen Tukur Buratai, ya gargadi kwandojin soji 70 da suka kara sanya ido domin mayakan Boko Haram sun koma neman mafaka a sauran sassan kasar.

Rundunar sojin Nijeriya a 'yan kwanakin nan, ta yi nasarar dakile yunkurin hare-hare ciki har da na kunar bakin wake da mayakan boko –haram suka shirya kai wa cikin birnin Maiduguri da kewaye. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China