A cewar Mohamed Adam, gwamnatin Sudan ta cika sharuddan da Amurka ta gindaya domin soke mata takunkumi, kuma an bude kashi 90 bisa dari na duk fadin yankin Sudan ga kungiyoyin kasa da kasa a halin yanzu.
Adam ya kuma ce, Sudan ta yi matukar kokari musamman ta fannin nuna jin-kai, ciki har da kai agajin jin-kai wuraren da suke fama da fadace-fadace, da saukaka ayyukan jin-kai, ta yadda ma'aikata masu samar da agajin za su isa yankunan dake fama da tashe-tashen hankali yadda ya kamata.(Murtala Zhang)