in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a ci gaba da sanya takunkumi kan Qatar
2017-07-12 12:05:26 cri

Duk da cewa, kasar Qatar da kasar Amurka sun sanya hannu kan wata takardar fahimtar juna game da yaki da yunkurin samar da taimakon kudi ga 'yan ta'adda, amma kasashe hudu wato Saudi Arabiya da Daular Larabawa da Bahrain da kuma Masar sun fitar da wata sanarwa cikin hadin gwiwa a jiya Talata, inda suka bayyana cewa, za su sa ido kan kasar ta Qatar domin duba ko za ta aiwatar da takardar yarjejeniyar da ta rattaba hannu a kai, kuma za su ci gaba da sanya mata takunkumi.

Sanarwar ta bayyana cewa, a cikin shekaru 3 da suka gabata, Qatar ba ta aiwatar da yarjejeniyar Riyad da ta daddale ba, har tana ci gaba da samar da kudade ga 'yan ta'adda, tare kuma da tsoma baki a cikin harkokin cikin gida na sauran kasashe, a saboda haka kasashen hudu sun gabatar da bukatu a fannoni 13 ga Qatar, idan Qatar ba ta iya biyan bukatunsu ba, to, za su katse huldar diplomsiyya da ita.

Wannan rana, bayan da kasashen biyu suka sa hannu kan takardar fahimtar juna, ministan harkokin wajen kasar Qatar Mohammed da takwaransa na kasar Amurka Tillerson sun shirya wani taron ganawa da manema labarai cikin hadin gwiwa, inda Mohammed ya bayyana cewa, kasarsa da Amurka sun sanya hannu kan takardar ne bisa tushen ci gaba da gudanar da hadin gwiwa tsakanin sassan biyu, lamarin ba shi da nasaba da rikicin katse huldar diplomasiyya, Tillerson shi ma ya bayyana cewa, Amurka za ta kara sanya kokari tare da Qatar domin kara karfafa hadin gwiwa dake tsakaninsu, ta yadda za su samar da tsaro ga al'ummar kasashen duniya yadda ya kamata.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China