Jean-Pierre Lacroix, mataimakin babban sakataran MDD mai kula da ayyukan wanzar da zaman lafiya shi ne ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga kwamitin tsaron MDD game da batun na jamhuriyar demokuradiyar Congo.
Game da batun tsaro, jami'in ya ce an samu tabarbarewar al'amurran tsaro ne galibin a yankunan kasar da dama, inda tashin hankali a lardin Kasai ya yi kamari.
Game da matakan da aka dauka a lardin na Kasai, tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD dake kasar Congo (MONUSCO), ta kakkafa kanana da cibiyoyin tafi da gidan ka a yankuna da dama domin tabbatar da tsaron rayukan fararen hula.
Sai dai kuma, duk da irin wadannan yunkuri, ana yawan samun rahotanni na cin zarafin bil adama kuma matsalar na cigaba da ta'azzara a kullum. (Ahmad)