in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Mozambick ya gana da ministan tsaron Sin
2017-07-12 10:42:41 cri

A jiya Talata ne shugaban kasar Mozambique Filipe Nyusi, ya gana da mamba a majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan tsaron kasar Chang Wanquan a fadar sa dake birnin Maputo.

Yayin zantawar ta su, shugaban Nyusi ya bayyana cewa, kasarsa na mai da hankali matuka kan huldar dake tsakaninta da Sin, kuma har kullum tana nacewa manufar "kasar Sin daya kacal a duniya", a hannu guda kuma za ta ci gaba, da kokarin karfafa cudanyar dake tsakanin kasashen biyu, a harkokin kasa da kasa da na shiyya-shiyya.

Kaza lika a cewar shugaban na Mozambique, gwamnatin sa na gabatar da babbar godiya game da taimakon da kasar Sin take samarwa gare ta a cikin dogon lokaci, tare da fatan karfafa hadin gwiwa da kasar ta Sin a fannin tsaron kasa.

A nasa bangare kuma, Chang Wanquan ya bayyana cewa, ziyarar da shugaba Nyusi ya kai kasar Sin a watan Mayun bara, ta taimaka matuka wajen ciyar da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu gaba, yana fatan ziyararsa a kasar Mozambique, za ta kara zurfafa zumuncin dake tsakanin al'ummomin kasashen biyu, tare kuma da bude wani sabon babi na huldar dake tsakanin sassan biyu, ganin cewa ita ma kasar Sin na mai da hankali sosai game da huldar hadin gwiwa tsakaninsu. (Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China