in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNFPA ta bukaci a kara zuba jari a fannin kula da shirin tsara iyali
2017-07-12 10:34:45 cri
Wata babbar jami'ar asusun kula da yawan jama'a ta MDD (UNFPA) a Ghana ta bukaci a kara zuba jari wajen kula da shirin tsara iyali a lokacin da ake gudanar da bikin rayar alumma ta duniya a birnin Accra.

Erika Goldson, ita ce mataimakiyar wakilin shirin na UNFPA, ta bayyana cewa baya ga batun kula da lafiya da hakkoki da ake samu, wadannan kudade da aka zubawa suna samar da bunkasuwar tattalin arziki da wasu muhimman al'amurran da za su haifar da cigaba kuma suna daga cikin muhimman nasarorin shirin nan na ajadanr samar da dawwamamman cigaba nan da shekara ta 2030 da kuma shirin 17 SDGs.

Goldson ta ce za'a samu nasarar kawar da kangin talauci, amma domin samun wannan nasara ana bukatar fahimtar dangantakar dake tsakanin tsara iyali da samar da daidaiton tsakanin jinsi da kuma bunkasuwar tattalin arziki.

Ta ce hakkin mata da yara yan mata na samun yancin yanke shawara game da yawan adadin 'yayan da suke son haifa zai kara ba su damammaki na samun ayyukan samun kudaden shiga, kuma hakan zai iya kara bunkasa samar karin kudaden shiga na iyalai da kyautata yanayin zamantakewa.(Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China