in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan da bukaci Amurka da ta dage mata takunkumin da ta saka mata baki daya
2017-07-11 19:10:47 cri
Ministan harkokin wajen kasar Sudan Ibrahim Ghandour ya bukaci gwamnatin kasar Amurka da ta dage mata dukkan takunkumin tattalin arzikin da ta kakabawa kasar

Ghandour ya ce duk wata shawara da kasar ta Amurka za ta yanke sabanin haka, hakika gwamnatin Sudan ba za ta lamunta ba kuma bai dace ba. Yana mai cewa, kasarsa ta cika dukkan sharuddan da Amurkan ta zayyana mata.

Ya ce, idan aka dage wa kasar takunkumin da aka kakaba mata yau kusan shekaru 21 da suka gabata, babu shakka Sudan za ta zama kawar Amurka a fannin tabbatar da tsaro a shiryya, kana hakan zai taimakawa al'ummomin kasashen biyu.

Tun a shekarar 1993 ne dai Amurka ta sanya Sudan cikin jerin kasashe dake taimakawa ayyukan ta'addanci, zargin da Sudan din ta musanta. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China