in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Al'ummar Sin suna jin dadin shiga jirgin kasa mai saurin tafiya
2017-07-11 10:49:51 cri

Layin dogon da aka gina domin jirgin kasa mai saurin tafiya na farko ya fara aiki ne a shekarar 2008 a nan kasar Sin, kawo yanzu, al'ummar kasar ta Sin sun saba, kuma suna jin dadin zirga zirga ta wannan jirgin kasa mai saurin tafiya wanda ke samar da hidima mai inganci ga fasinjoji.

A tashar saukar jirgin kasa ta kudu dake nan birnin Beijing, fasinjoji da dama suna tafiya cikin sauri domin shiga jirgin kasa, ko wace rana akwai jiragen kasan da yawansu ya kai 318 ne suke fitowa daga tashar, domin tafi wurare daban daban a fadin kasar ta Sin.

Gyatuma Zhu Yunxia tana da shekarun haihuwa 82 a bana, ga ta can take fitowa daga jirgin kasan da ya sauka nan birnin Beijing daga birnin Shanghai dake kudancin kasar Sin, ga alama tana jin dadi, babu gajiya ko kadan, ta gaya mana cewa, "Kafin tashina daga gida na dake Shanghai, yarana sun nuna damuwa saboda zan shiga jirgin kasa ni kadai, amma na gaya musu cewa, babu matsala, sauran fasinjoji da dama su ma hakan ne ra'ayin su, kana wasu matasa su kan taimakawa saura, musamman ma tsoffi, shi ya sa ban ji gajiya ba ko kadan. Ko shakka ba bu ina jin dadin shiga jirgin kasa mai saurin tafiya, ina kuma ganin cewa, ya fi jirgin sama, saboda wurin zama a cikin jirgin kasa ya fi na jirgin sama girma."

Yawancin fasinjoji sun fi so su shiga jirgin kasa mai saurin tafiya ne bisa dalilin hidima mai inganci, hakika, wani dalili daban da ya sa haka shi ne domin sau kadan ne jirgin kasa ke makara. Gyatuma Zhu Yunxia ta bayyana cewa, "Idan ana son shiga jirgin sama, to dole ne a isa filin jirgin sama kafin lokaci tashi da awa biyu ko fiye, gaskiya hakan ba dadi, kana idan yanayi ba kyau, a kan jinkirta tashin jirgin sama, wani lokaci kuwa, a kan soke shi. mun tsufa, mun fi jin damuwa, shi ya sa na fi son shiga jirgin kasa mai saurin tafiya a maimakon jirgin sama."

Yanzu a kasar Sin, adadin fasinjojin dake tafiya tsakanin biranen Beijing da Shanghai ya karu. Layin dogon jirgin kasa mai saurin tafiya ya fara aiki ne tun daga watan Yunin shekarar 2011, tsayinsa kuma ya kai kilomita 1318. A ko wace rana, adadin jirgin kasa dake tafiya tsakanin biranen biyu ya kai 320, da haka adadin fasinjojin da suka shiga wadannan jiragen kasa a shekarar bara ya kai miliyan 100.

Malam Chen, wani ma'aikaci ne dake aikin harkar kudi, ko wane sati, ya kan shiga jirgin kasa dake tsakanin birnin Beijing da garin Wuqing na birnin Tianjin sau da dama, domin gudanar da aikinsa, tazarar dake tsakanin Beijing da Wuqing ta kai kilomita kusan 90, idan za a bi hanyar mota, ana bukatar awa guda ko fiye, amma in aka shiga jirgin kasa mai saurin tafiya, to, ana bukatar minti 24 ne kacal. Malam Chen ya gaya mana cewa, "Shiga jirgin kasa mai saurin tafiya zai rage lokacin tafiya kan hanya, kana idan ka tuka mota, kila ka gamu da cunkuso, musamnan ma a cikin unguwanin birnin, kana kudin da za a kashe kan tafiyar zai ragu idan ka shiga jirgin kasa mai saurin tafiya a maimakon tuka mota."

Kafin shekarar 2008, garin Wuqing karamar unguwa ce dake birnin Tianjin, amma bayan da layin dogon jirgin kasa mai saurin tafiya ya fara aiki, sai adadin fasinjojin da suke shiga garin ya karu zuwa miliyan 4 a shekarar 2016, hakan ya samar da damammaki da yawa na ci gaban tattalin arzikin wurin. Malam Chen shi ma ya ga manyan sauye-sauyen da suka faruwa a garin da idanunsa, ya ce, "Bayan da layin dogon jirgin kasa mai saurin tafiya dake zirga zirga tsakanin Beijing da Wuqing ya fara aiki, sai 'yan kasuwan da suke zuwa garin domin zuba jari ya karu, haka kuma masu yawon bude ido da suke zuwa wurin su ma sun karu, a saboda haka, garin ya samu ci gaba cikin sauri."

Kazalika, sha'anin yawon bude ido a fadin kasar Sin shi ma ya samu bunkasuwa a bayyane, tun bayan da aka fara gina layin dogon jirgin kasa mai saurin tafiya a shekarar 2008, saboda yanzu ana iya tafiya zuwa sauran wurare ne cikin sauri da kuma cikin sauki.

Al'ummar kasar Sin suna ganin cewa, shiga jirgin kasa mai saurin tafiya yana da tsaro, kuma suna jin dadin, a shekarar 2016, adadin fasinjojin da suka shiga jirgin ya kai biliyan 1 da miliyan 440.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China