in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNAMID ta ce ana samun ingantar yanayi a yankin Darfur
2017-07-11 10:33:52 cri

Tawagar hadin gwiwar MDD da kungiyar AU mai aikin wanzar da zaman lafiya a yankin Darfur na kasar Sudan ko (UNAMID) a takaice, ta ce al'amuran tsaro da na jin kai na kara kyautata a yankin Darfur. Sai dai kuma a hannu guda tawagar ta ce, har yanzu akwai sauran rina a kaba, game da kudurorin da ake fatan a cimmawa, don gane da wanzar da zaman lafiya da lumana a yankin.

Babban jami'in musamman na tawagar ta UNAMID Jeremiah Mamabolo, shi ne ya shaidawa taron manema labarai hakan, yana mai cewa, a yanzu, tashe tashen hankula tsakanin dakaru masu dauke da makamai, ya takaita ne ga kungiyar 'yan tawayen "Sudan Liberation Army" tsagin Abdul Wahid dake ayyukan ta a yammacin Jebel Marra.

Sai dai duk da ci gaban da ake samu, Mr. Mamabolo ya ce akwai kimanin mutane da yawan su ya kai miliyan 2.7 da suka rasa matsugunnan su, wadanda a yanzu ke samun mafaka a wasu sansanonin 'yan gudun hijira. Har ila yau wasu mayakan sa kai na kaddamar da hare hare masu nasaba da kabilanci a sassa daban daban na yankin.

Daga nan sai Mamabolo ya bayyana bukatar daukar matakai cikin nutsuwa, domin dakile yaduwar rigingimu, da wanzar da zaman lafiya mai dorewa. Ya ce, yanzu haka suna tsaka da gudanar da ayyuka masu nasaba da inganta ayyukan tawagar su, kamar dai yadda hakan ke kunshe cikin kudurin kwamitin sulhun MDD mai lamba ta 2363, wanda ya bukaci a aiwatar da hakan.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China