in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar zaben Somalia na rajistar jam'iyyun siyasa gabanin zaben 2021
2017-07-11 10:29:17 cri

Hukumar zaben kasar Somalia mai zaman kan ta NIEC, ta fara gudanar da rajistar jam'iyyun siyasa a kasar, gabanin zaben kasar dake tafe cikin shekara ta 2021

Da take tabbatar da hakan a jiya Litinin, shugabar hukumar Halima Ibrahim, ta ce yanzu haka hukumar tana hadin gwiwa da sauran abokan hulda daban daban, domin fidda managarcin tsarin da zai inganta ayyukan jam'iyyun kasar, ta hanyar yi musu rajista da samar masu da kudade, gabanin zaben kasar mai tunkarowa.

Halima Ibrahim ta ce, yi wa jam'iyyu rajista, daya ne daga ginshikan da ake bukata na ganin ko wane 'dan kasar ya samu damar kada kuri'a daya tak kamar yadda doka ta tanada.

Jami'ar wanda ta bayyana hakan yayin wani taron yini uku na inganta sanin makamar aiki wanda ya gudana a birnin Nairobin kasar Kenya, ta kara da cewa, gwamnatin Somalia na da burin ganin ta samu karin kwarewa daga sassan masu ruwa da tsaki, karkashin tsarin ta na hadin gwiwa da kasashen nahiyar Afirka, da na Larabawa, game da dabarun farfado da jam'iyyu, bayan tashe tashen hakula na tsawon shekaru da suka addabi kasar.

Ofishin tallafawa harkokin zabe na MDD IESG ne ya dauki nauyin shirya wannan taro, da hadin gwiwar takwaransa na tarayar Larabawa da kuma hukumar UNDP.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China